Isa ga babban shafi
Afghanistan-Nato-Amurka

Taliban ta sanar da janye wa daga Kunduz

Kungiyar Taliban ta sanar da janye wa daga birnin Kunduz dake kasar Afghanistan, makwanni biyu bayan kama birnin dake arewacin kasar.

Mayakan Taliban
Mayakan Taliban REUTERS/Stringer
Talla

Sanarwar da kungiyar ta saka a kafar intanet ta ce, ta umurci mujahidinta da su janye daga dandalin garin, kasuwanni da gine ginen gwamnati domin kare makamanta da kuma rayukan fararen hula.

Mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid ya ce, kungiyar na da karfin da za ta iya sake karbe ikon birnin na Kunduz matukar ta bukaci haka.

Sojojin gwamnatin kasar da ke samun taimakon jiragen sama na kungiyar tsaro ta NATO na farautar mayakan da suka rage a birnin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.