Isa ga babban shafi
Kamaru

"Uwargidan Biya ce ke mulki a Kamaru"

Kafafen yada labarai na cigaba da bayyana Uwargidan shugaban kasar Kamaru Chantal Biya a matsayin mai karfin fada a-ji, wacce kuma ke taka gagarumar rawa wajen nada muhimman mukamai a gwamnatin Shugaba Paul Biya.

Shugaban Kamaru Paul Biya da uwargidansa, Chantal Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya da uwargidansa, Chantal Biya BRENDAN SMIALOWSKI / AFP
Talla

Kafafen yada labaran da suka hada da jaridar Jeune Afirque, sun bayyana cewa tasirin Chantal Biya wajen nada muhimman mukamai ya wuce misali, domin kuwa hatta sakataren gwamnati, Ferdinand Ngoh Ngoh da kuma shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasar ita ce ta yi ruwa da tsaki domin tabbatar musu da mukaman.

Jeune Afrique ta gudanar da bincike ne wanda kuma sakamakonsa ya fito a wannan Litinin, in da ya nuna yadda matar shugaban ke da karfin fada aji fiye da yadda ake zato.

Jaridar ta ce, shugaba Paul Biya da kansa, na kiran ta ne da suna Yah Ke "Mai girma shugaba", duk da cewa ba wani matsayi mai kama da hakan a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Mafi yawan mutanen da jaridar ta zanta da su na cewa a halin yanzu matar shugaban ta shiga gadan-gadan a lamurran da suka shafi siyasar kasar, yayin da jama’a ke kamun kafa a wajenta domin samun mukami ko kuma kwangila a gwamnati.

Manazarta dai na danganta hakan ne watakila ko dai saboda yarda ko kuma tsufan shugaba Paul Biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.