Isa ga babban shafi
Kamaru

An rantsar da shugaba Biya wa'adi na bakwai a Kamaru

An rantsar da shugaban kasar Kamaru, Paul Biya wa’adi na bakwai kan karagar mulki bayan nasarar da ya samu a zaben da ya gabata da kashi 71.

Shugaban Kamaru Paul Biya ya lashe zaben da gagarumin rinjaye
Shugaban Kamaru Paul Biya ya lashe zaben da gagarumin rinjaye AFP
Talla

Shugaba Biya mai shekaru 85 da ya kwashe shekaru 36 a karagar mulki, ya yi alkawarin tabbatar da gaskiya da kuma adalci a fadin kasar.

Shugaban ya yi kuma tsokaci kan 'yan aware wadanda ke fafutukar raba kasar ta hanyar tashin hankali da kuma kaddamar da munanan hare-hare.

Kwana guda kafin shan rantsuwar ci gaba da zama a karagar mulkin, 'Yan awaren sun kaddamar da wani hari a yankin Bamenda, in da suka yi awon gaba da dalibai 79 tare da malaminsu da shugaban makarantar da kuma direba.

A shekarar 2016 aka fara bore a yankin kasar da ke amfani da Turancin Ingilishi kan korafi kan yadda ake bada ilimi da bangaren shari’a da kuma tattalin arziki, ganin yadda Yankin Arewa Maso Yamma da Kudu Maso Yamma ke fama da matsaloli.

Wannan ne ya sa masu fafutukar bayyana kafa kasar Ambazonia da kuma daukar makamai, abin da ya yi sanadiyar kai munanan hare-hare akan jami’an tsaro da sojoji wanda ya kai ga kashe fararen hula sama da 400 da kuma jami’an tsaro akalla 175.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.