Isa ga babban shafi
Kamaru-Amurka

Zaben Kamaru na cike da kura-kurai- Amurka

Amurka ta ce an tafka kura-kurai da dama a zaben shugabancin kasar Kamaru wanda hukumar zabe ta bayyana Paul Biya a matsayin wanda ya yi nasara da kimanin 71%.

Shugaban Kamaru, Paul Biya lashe zaben don jagorancin kasar a karo na bakwai
Shugaban Kamaru, Paul Biya lashe zaben don jagorancin kasar a karo na bakwai REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar wajen Amurka Heather Nauret, ta ce tabbas an dan samu ci gaba ta fannin tsara zabe idan aka kwantanta da wanda aka yi shekara ta 2011 a kasar, to amma an samu kura-kurai da dama a wannan karo.

Shugaba Biya da ya dare kan karagar mulkin Kamaru tun shekarar 1982, ya sake lashe zaben ne da gagarumin rinjaye kamar yadda sakamakon da aka fitar a ranar Litinin ke nuna.

Gwamnati ta girke jami’an tsaro a babban birnin kasar, yayin da aka ji karar harbe-harben bindiga a yankin masu magana da Turanci Ingilishi mai fama da rikici.

Kotun Fasalta Kundin Tsarin Mulkin Kamaru da makusantan shugaba Biya suka mamaye ta, ta bayyana cewa, shugaban ya lashe zaben da kashi 71.3 na kuri’un da aka kada a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Shugaban Kotun, Clement Atangana, ya ce, babban dan adawar Biya a zaben, wato Maurice Kamto, shi ne ya yi na biyu da kashi 14.2 na kuri’un da aka kada.

Kotun ta samu kwanaki 15 bayan gudanar da zaben don sauraren korafe-korafen bayan zabe, in da ta yi watsi da dukkanin korafe-korafe 18 da aka shigar a gabanta, yayin da a yanzu babu wanda ya isa ya kalubalanci sakamakmon karshe.

Biya ya lashe zaben ne duk da zarge-zargen tafka magudi da karancin fitowar masu kada kuri’u har ma da barkewar rikici a yayin gudanar da zaben na Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.