Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2018

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2018 makwanni da dama bayan majalisar kasar ta amince da shi.Dama tun a jiya Talata mai magana da yawun shugaban Mr Femi Adesina, ya ce Muhammadu Buhari zai sanya hannu kan kasafin da misalin karfe 12 na ranar yau Laraba.

Bayan shafe makwanni da dama da sahalewar majalisar Najeriya kan kunshin kasafin kudin kasar a yau Laraba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kunshin kasafin.
Bayan shafe makwanni da dama da sahalewar majalisar Najeriya kan kunshin kasafin kudin kasar a yau Laraba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kunshin kasafin. REUTERS/Stringer
Talla

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da tsakar ranar yau Laraba, ya ce ya sanya hannu kan kasafin kudin na shekarar 2018.

Rahotanni sun shugaban ya sanya hannun ne a ofishinsa na da ke fadarsa ta Villa a Abuja babban birnin kasar.

Sai dai shugaban ya nuna damuwa matuka kan wasu sauya-sauye da ya ce Majalisar kasar ta aiwatar a kunshin kasafin na 2018.

Muhammadu Buhari ya ce bai ji dadin yadda majalisar ta rage kasafin da kusan Naira biliyan dari uku da hamsin na wasu ayyuka dubu 7 da dari 7 yayinda suka gabatar da wasu ayyuka dubu 6 da 403 na kashin kansu da zai lakume Naira biliyan dari biyar da 78.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.