Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya ta amince da kasafin kudin 2017

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kasafin kudin 2017 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika a karshen shekarar 2016. Rahotanni sun ce majalisar ta yi karin kudi kusan biliyan160 daga kasafin da Buhari ya aika.

Majalisar dokokin Najeriya
Majalisar dokokin Najeriya facebook
Talla

Buhari ya yi kasafin kudin ne na 2017 na Naira Tiliyan 7.28.

A karon farko Majalisar ta ce za ta fayyace kasafin kudinta sabanin baya da ba a saba saba bayyana kasafin kudin majalisun guda biyu ga 'yan kasa.

Amma Majalisar ta kara kasafin kudinta daga Naira Biliyan 100 zuwa Biliyan 125 a kasafin kudin na 2017.

A Kasafin na 2017 an ware wa hukumar Neja Delta kudi Naira Biliyan 64.02, Ilimin bai-daya na UBE Naira biliyan 95.2, hukumar zabe Naira biliyan 45.

Kudi Naira biliyan 100 aka warewa Majalisar Alkalai, hukumar kare hakkin bil’adama kuma Naira biliyan 1.2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.