Isa ga babban shafi
Najeriya

Cuwa-cuwar da majalisar Najeriya ta yi a kasafin kudi

Wasu takardu sun fallasa yadda mambobi majalisar wakilan Najeriya suka yi kokarin almundahana a shirin kasafin kudin shekarar 2016, inda suka ware wa kansu kazaman kudade don gudanar da ayyukan karya a mazabunsu kamar yadda jaridar Premium Times ta kasar da ake wallafawa a shafin Intanet ta rawaito.

Mambobin majalisar wakilan Najeriya
Mambobin majalisar wakilan Najeriya Reuters
Talla

Jaridar ta ce, an aiko ma ta da takardun ne a yayin da tayar da jijiyoyin wuya ta tsananta a tsakanin ‘yan majalisar dangane da badakalar kasafin kudin.

Majalisar ta tsindima cikin rudani sakamakon tsige Hon. Abdulmumin Jibrin daga mukaminsa na shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a majalisar.

Shugaban majalisar, Yakubnu Dogara ya ce, Jibrin ya ci amanar da abokan aikinsa suka ba shi.

Sai dai, Hon Jibrin ya musanta zargin inda ya ce, Dogara ne ya yi kokarin shigar da biliyoyin kudi cikin kasafin na 2016.

Takardun da jaridar Premium Times ta samu a jiya Lahadi, sun nuna yadda mambobin majalisar suka bukaci Dogara da ya sanya musu hannu don gudanar da ayyukan karya daban-daban a mazabunsu, da suka hada da gina burtsatse a jihar Kano da kuma ciyar da masu samun horon aikin ‘yan sanda a Bauchi.

Takardun dai sun nuna cewa, Dogara ya sanya hannu don amince wa da ayyukan ba tare da fitar da filla-fillan bayanai game da yadda za a kashe kudaden ba, abinda ke nuna cewa, ‘yan majalisar na bukatar cika aljihunsu ne kawai amma ba gudanar da wani aiki a wata mazaba ba kamar yadda Jaridar Premium times ta rawaito.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.