Isa ga babban shafi
Najeriya

Zamu ci gaba da bankado badakalar da PDP ta aikata - Yemi Osinbajo

Gwamnatin Najeriya ta ce ya zama dole a ci gaba da shaidawa al’ummar kasar irin matsalar da aka fuskanta a baya na satar dukiyar kasa wadda ta kai ga jefa al’ummar ta cikin kunci.

A cewar mataimakin shugaban Najeriyar ba cikin sauki al'ummar kasar za su manta da irin bannar da jam'iyyar ta PDP ta tafka ba.
A cewar mataimakin shugaban Najeriyar ba cikin sauki al'ummar kasar za su manta da irin bannar da jam'iyyar ta PDP ta tafka ba. Solacebase
Talla

Yayin jawabi wajen bikin cika shekaru 66 na jagoran Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da aka gudanar yau a Lagos, mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osibanjo, ya ce abin takaici ne irin satar da gwamnatocin da suka gabata suka yi.

Taron na yau wanda ya tattaro kusan dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren siyasa da tattalin arziki da kuma masarautun Najeriya, ya mayar da hankali kan yunkurin da gwamnati mai ci keyi wajen magance matsalar yaki da cin hanci da rashawa da kuma gina matasa.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce babu wani mai kishin kasa da zai ga irin satar dukiyar da akayi ba tare da hankalin sa ya tashi ba.

Osinbajo ya kuma bukaci 'yan Najeriya kan kada su yarda su amince da neman yafiyar da PDP ke yi yana mai cewa ta hakan ne ta ke neman gurbin sake komawa kan mulki don ci gaba da wargaza Najeriyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.