Isa ga babban shafi

Shugabancin jam'iyyar PDP ya rasa tudun dafawa - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana shugabancin jam’iyyar adawa ta PDP da cewa tamkar wadanda ke kokarin nutsewa ne cikin ruwa, don haka zasu iya kama duk abinda suka samu, ko aka mika musu, don tsira da ransu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS /Stringer
Talla

Cikin sanarwar da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce matakin da jam’iyyar ta PDP ta dauka, na shigar da karar hukumar shirya zabukan kasar INEC da jam’iyyar APC mai mulki, zuwa a gaban majalisar dinkin duniya, bisa zarginsu da shirya tafka magudi a zaben 2019, abin dariya ne da takaici.

A cewar shugaban Najeriya, hakan yana nuni da cewa jam’iyyar ta PDP tana shakkar fuskantar masu kada kuri’a ne a lokacin zabukan na 2019.

Sanarwar ta kuma ce, zabukan gwamna a jihohin Anambra, Edo da Ondo kyawawan misalai ne da ke nuna cewa gwamnatin Najeriya bata da wata mummuniyar aniya a zabukan masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.