Isa ga babban shafi
Liberia

Zaben Liberia: Gwamnati ta musanta tattaunawa da Weah

A dai dai lokacin da ake dakon matakin kotun kolin Liberia kan zaben shugabancin kasar, rahotanni daga kasar sun ce, an shiga tattaunawa tsakanin magoya bayan shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf, da jam’iyyar dan takara George Weah kan kada ya bincike wasu al’amura idan yayi nasarar zama shugaba.

Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf a fadar gwamnati da ke babban birnin kasar Monrovia. 12 ga Oktoba, 2017.
Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf a fadar gwamnati da ke babban birnin kasar Monrovia. 12 ga Oktoba, 2017. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Sai dai a wani yanayi na samun rahotanni masu cin karo da juna, wani na hannun damar shugaba Sirleaf ya musanta hakan.

Al’amarin na boye ya fito fili ne bayanda wani tsohon jami’in bincike a wata kotu ta musamman a Saliyo, dan kasar Amurka Alan White ya sanar da haka.

A wata ganawa da jaridar la voix daga Amurka, Alan White ya ce dan takara George Weah ya amince muddin ya lashe zaben, zai yi watsi da duk wani batun bincike kan gwamnatin Ellen Johnson Sirleaf dama soke du kuma soke duk wata tuhuma kan batutuwa da suka shafi cin hanci da rashawa.

Bangaren jam’iyyar dan takara George Weah ba su ce komai kan batun ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.