Isa ga babban shafi
Liberia

Zaben Liberia: George Weah da Joseph Boakai zasu fafata a zagaye na 2

Hukumar zabe a kasar Liberia ta bayyana cewar tsohon tauraron kwallon kafar kasar George Weah zai fafata da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai a zabe zagaye na biyu da za’ayi ranar 7 ga watan gobe.

Dan takarar shugabanci Liberia George Weah
Dan takarar shugabanci Liberia George Weah ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Shugaban hukumar zabe Jerome Korkoya ya ce alkaluman zaben da aka tattara a kashi sama da 95 na mazabun kasar sun nununa cewar, George Weah ya samu kashi 39 na kuri’un da aka kada, yayin da Boakai ya samu kashi 29.

Korkoya ya ce kashi sama da 74 na masu kada kuri’u suka shiga zaben, kuma ganin yadda babu wanda ya samu kashi 50, yanzu za’a aje zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.