Isa ga babban shafi
Liberia

An fara kada kuri'u a zaben shugaban kasa a Liberia

Al’ummar Liberia sun isa rumfunar zabe a wannan Talata don kada kuri’a a zaben shugaban kasa da zai maye gurbin uwargida Ellen Johnson Sirleaf.

An fara kada kuri'a a zaben shugabancin kasar Liberia
An fara kada kuri'a a zaben shugabancin kasar Liberia Reuters/Thomas Mukoya
Talla

Zaben wanda aka fara da misalin karfe takwas 8 na safe agogon kasar, za a kammala shi da misalin karfe karfe shida na yammma.

A karon farko cikin shekaru 70 za a mika mulki ta hanyar demokradiya a kasar Liberia mai yawan al’umma miliyan 2.18.

‘Yan takara 20 ne ke fafatawa a zaben da suka hada da tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar, Gorge Weah da mataimakin shugaban kasa, Joseph Boakai da wani fitaccen dan adawa, Charles Brumskine, sai kuma wata mace guda.

Ana saran fitar da sakamkon farko a hukumance cikin sa’oi 48, amma matukar aka gaza samun dan takara guda da ya lashe kashi 50 cikin 100 na kuri’un, to lallai za a je ga zagaye na biyu na zaben a ranar 7 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Da dama daga cikin masharhanta kan siyasar Liberia na ganin cewa, mawuyaci ne ba a kai ga zagaye na biyu ba.

A wani takaitaccen jawabi da ta gabatar wa al’ummar kasar, shugabar kasar mai barin gado, Ellen Johnson Sirleaf ta bukaci jama’a da su mutunta sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.