Isa ga babban shafi
Liberia

Zaben Liberia: Kotu zata yanke hukunci ranar Litinin

Kotun kolin kasar Liberia, ta ce sai a ranar Litinin zata yanke hukunci kan yiwuwa ko akasin haka na gudanar da zaben shugabancin kasar zagaye na biyu kamar yadda aka tsara a ranar 7 ga wannan wata.

Ginin kotun kolin kasar Liberia da ke babban birnin kasar Monrovia.
Ginin kotun kolin kasar Liberia da ke babban birnin kasar Monrovia. REUTERS/James Giahyue
Talla

Za dai a fafata ne tsakanin shahararren dan kwallon kafa George Weah da ya fi lashe kuri’u a zagayen farko da kuma mataimakin shugaban kasa mai ci, Joseph Boakai, wanda ya marawa ‘yan adawar da suka garzaya kotu dan neman a soke zaben saboda zargin aikata magudi.

Matakin kotun ya sa masu sa’ido na cikin gida da kasashen ketare bayyana shakku kan ko zaben shugabancin kasar, zai gudana kamar yadda aka tsara a ranar 7 ga watan da muke ciki.

A ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata, kotun kolin Liberia ta bai wa hukumar shirya zaben kasar umarnin dakatar da shirin gudanar da zagaye na biyu na zaben da aka shirya za'ayi a ranar 7 ga watan Nuwamba, domin bata damar sauraron koken da jam'iyyun adawa da mai mulki suka gabatar mata na zargin an aikata magudi a zaben shugabancin kasar, zagaye na farko da George Weah yafi samun kuri'u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.