Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta wanke Okah daga laifin cin amanar kasa

Lauyoyin da ke kare Charles Okah wanda ake zargi da kitsa harin bam da aka kai ranar 1 ga watan oktoban 2010 a birnin Abuja, sun bayyana gamsuwarsu da matakin da kotu ta dauka na yin watsi da daya daga cikin zarge-zargen da ake yi masa saboda rashin gabatar da hujjojin da ke tabbatar da wanda ake zargi na da hannu a lamarin.

Charles-Okah, dan Najeriya da ake zargi da kai harin bam ranar 1 ga watan oktoban 2010 a Auja
Charles-Okah, dan Najeriya da ake zargi da kai harin bam ranar 1 ga watan oktoban 2010 a Auja
Talla

Lauyan Okah Alex Izinyon, wanda ke magana da manema labarai jim kadan bayan da kotu ta sanar da yin watsi da karar, ya ce laifufuka biyu da ake zargin wanda yake karewa, wato cin amanar kasa da kuma ta’addanci, amma sun yi nasara a kan daya daga cikinsu, kuma sauran zance ya rage a hannun mai shigar da kara na gwamnati.

Charles Okah da kuma wani mai suna Obi Nwabueze, ana zarginsu da hannu a wani harin da aka kai ranar 15 ga watan maris na 2010 a garin Warri na jihar Delta, inda ake tuhumarsu da yunkurin kashe tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da kuma wasu gwamnoni da ke taro a jihar ta Delta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.