Kotu ta yankewa Henry Okah hukuncin daurin shekaru 24
Wata kotu a kasar Afrika ta Kudu ta yanke wa Henry Okah, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 24, mutumin da ake zargi da kai harin bam a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya a shekarar 2010. An yanke wa Okah hukuncin bayan kotun ta same shi da laifuka 13 da suka hada da ayyukan ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 a harin bam din na Abuja.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
“A dalilin haka ne, aka yankewa Okah hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 24.” Inji Alkali Neels Claassen.
Mutane 12 ne suka rasa rayukansu a lokacin da bama-baman suka tashi, a dai dai lokacin da ake bikin cika shekaru 50 da samun ‘yanci kai a Najeriya.
A lokacin karar an yi zargin cewa, Okah bai nuna cikakkiyar nadama ba akan abin da ya aikata, domin a cewar rahotanni, ainihin nufinsa shi ne a samu hasarar rayuka da dama kamar yadda rahotanni suka nuna.
Kungiyar fafutuka ta neman ‘yancin yankin Niger Delta da aka fi sani da MEND a takaice wacce Okah ya ke jagoranta, ta dauki alhakin harin a lokacin, sai dai Okah wanda mazauni ne a kasar ta Afrika ta Kudu na dindindin, ya musanta zargin cewa yana da hanun a harin, inda ya ce an alakanta shi da harin ne saboda siyasa.
Har ila yau kotun ta same shi da laifin saka hanu a wasu hare-hare da aka kai guda biyu a garin Warri da ke kudancin Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu