Chinua Achebe, marubuci a Najeriya ya mutu
Shahararren marubucin Najeriya Chinua Achebe, masanin adabi ya mutu yana shekaru 82. Chinua Achebe, ya yi suna a Afrika saboda littafin da ya rubuta mai taken "Things Fall Apart," wanda ke da jigon yadda bakaken fata suka sha wahala ga turawan mulkin mallaka a karni na 1800.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Chinua Achebe, ya mutu ne a wata asibiti a Massachusetts kasar Amurka. Kamar yadda Mari Yamazaki kakakin kamfanin buga littafi na Penguin ta tabbatarwa kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP.
Achebe ya yi fice ne a duniya saboda Littafinsa da ya rubuta mai taken "Things Fall Apart," wanda ke bayani game da yadda Turawan Ingila suka yi mulkin Mallaka da kuma al’adun kabilar shi ta Igbo a kudancin Najeriya.
Achebe ya dade yana adawa da matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya, lamarin da ya gurgunta tattalin arzikin kasar.
Amma Achebe ya goyi bayan yakin Biafra na Kabilar Igbo da ya lakume rayukan mutane kusan Miliyan a shekarar 1967-1970 a lokacin da suka nemi ballewa daga Najeriya.
A shekarar 2011 Achebe ya yi watsi da lambar yabon da gwamnatin Najeriya za ta ba shi wanda shi ne karo na biyu.
Achebe ya kwashe shekaru da dama a kasar Amurka a matsayin Farfesa a Jami’ar Brown a Rhode Island.
Wata marubuciyar Afrika ta Kudu ta bayyana Achebe a matsayin Uban Adabi a Afrika a lokacin da zai karbi wata kayutar Adabi ta Duniya.
Yana da wahala Dalibin sashen Turanci ya kammala karatu ba tare da ya karanta littafin Achebe ba, musamman a Najeriya.
Sai dai kuma Achebe bai taba lashe kyautar Nobel ba a fannin adabi kamar yadda Wole Soyinka,ya lashe kyautar a shekarar 1986.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu