Isa ga babban shafi
Najeriya

Soyinka ya bukaci al’ummar kudancin Najeriya kaucewa daukar fansa

Fitaccen Marubucin Najeriya wanda ya karbi kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya bukaci al’ummar Kudancin kasar Najeriya kaucewa mayar da martani ga ‘Yan Arewa da sunan daukar fansa, sakamakon hare haren da kungiyar Boko Haram ke yi.

Wole Soyinka, Fitaccen Marubucin Najeriya wanda ya karbi kyautar Nobel a shekarar 1986
Wole Soyinka, Fitaccen Marubucin Najeriya wanda ya karbi kyautar Nobel a shekarar 1986 DR
Talla

A wata ganawa da Soyinka ya yi da manema labarai a birnin Lagos, Farfesan yace, yanzu lokaci ne na ganin kowa ya kare makwabcinsa, ko daga kasar waje ya fito, balantana Arewacin Najeriya.

A nasa bangaren Babban Hafsan sojin kasar, Air Marshall Oluseyi Petirin, ya bukaci taimakon al’ummar kasar wajen samun bayanan siri domin magance matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.

Mista Petirin, ya yi watsi da ikrarin ‘Yan kabilar Igbo da ke cewa mutanensu ake kashewa a Arewacin kasar.

A lokacin da yake ganawa  da manema labarai bayan harin Kano da ya lakume rayukan mutane 185, Petirin ya bayyana cewa kashi 99 na adadin mutanen da suka mutu a Kano, al’ummar Musulmi ne, don haka shi ke nuna ba rikicin adddini bane illa wata manufa ta wadanda ke kai hare haren.

A makon jiya ne ranar Juma’a aka kai hari a birnin Kano wanda ya hallaka rayukan mutane 185.

Sai dai da safiyar yau Talata a birnin na Kano an sake jin karar bama bamai a daidai ofishin ‘Yan sanda da aka kai hari a makon jiya.

Masana dai sun hasashen kungiyar Boko Haram da ake zargin kaddamar da hare hare a Arewacin Najeriya ta rabu ne gida da yawa, inda ake zaton bangarorin kungiyar suna da manufofinsu iri daban daban.

Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin Kirsimeti wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 45 da harin watan Ogusta da aka kai a ginin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya janyo hasarar rayukan mutane 25.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.