Shugaban Najeriya yace an cafke wasu da ake zargin sun kai hari a Kano
Shugaban Najeriaya Goodluck Jonathan yace an cafke wasu da ake zargin sun kai hari a birnin Kano wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 178, tare da jaddada ci gaba da farautar ‘Yan kungiyar Boko Haram.A cewar shugaban Jonathan akwai wasu dake daukar nauyin su, domin a ko ina a duniya akwai wasu da ke daukar nauyin aikin ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Ziyarar shugaban na zuwa ne kwanaki biyu bayan wata musayar albarussai da harin bom da aka kai a birnin Kano bayan kammala sallar Juma’a.
Tun fara mulkin Jonathan a Najeriya yake fuskantar kalubale da rikicin Boko Haram wanda ke kokarin jefa kasar cikin yakin basasa.
Shugaba Jonathan ya kai ziyara wuraren da aka kai hare haren da kungiyar boko Haram ta yi ikirarin daukar nauyi da suka hada da hedikwatar ‘Yan sanda.
Shugaban ya gana da Sarkin Kano mai Martaba Ado Bayero, inda yake cewa aikin ta’addanci ga wani mutum daya ya shafi al’umma baki daya.
Bayan kai harin Bom a garin kano an sake samun rikici a bangaren Arewacin Najeriya, inda mutane 10 suka mutu bayan musayar wuta a garin Tafawa Balewa a Jahar Bauchi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu