Isa ga babban shafi
Najeriya

Tashin Hankali da Zaman Zullumi na karuwa cikin Arewacin Najeriya

Yayin da adadin wadanda suka hallaka sakamakon hare hare bama bamai a garin Kano suka haura 150, rohotanni da safiyar yau Lahadi na nuna da cewa an kaddamar da wasu hare haren kan garin Tafawa Balewa dake Jihar Bauchi, inda yanzu mutane ke tsarewa. 

Reuters
Talla

Babu cikekken rohoto kan wadanda abun ya ritsa dasu a garin na Tafawa Balewa, amma ana cikin halin rudu da rudani, kuma babu wani jami'i da ya tantance abunda ke faruwa. Amma wasu rohotanni sun ce 'yan sanda sun samu galba kan maharan.

Tashe tashen bama bamai da harbe harbe da suka ratsa birnin Kano na Tarayyar Nigeria, sun hallaka akalla fiye da mutane 150.

Yanzu haka an sassauta dokar hana fita na dare da rana, kuma jaridun kasar sun ruwaito kungiyar Boko Haram mai dauke da makamai tana daukan alhakin kai hare haren.

Ankai hare haren kan ofisoshin ‘yan sanda da wasu gine ginen gwamnati.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.