Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake jin karar bama bamai da musayar albarussai a Kano

A garin Kano an sake jin karar bama bamai a safiyar talata daidai da ofishin ‘yan sanda da aka kai hari a makon jiya da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 185.An ji karar fashewar bama bamai 15 da harbin bindiga a harabar Hedikwatar ‘Yan sanda, sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani game da sabon harin.

Harin ranar juma'a da aka kai a garin Kano
Harin ranar juma'a da aka kai a garin Kano REUTERS
Talla

Wani shaidun gani da ido ya shaidawa kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa Jami’an tsaro ne suka kai wani samame a wani gida da ake zargin mabuyar ‘yan Kungiyar boko Haram ne. anan take ne aka fara musayar wuta na tsawon sa’o’I hudu da rabi.

A cewar shaidun ya ga gawar mutane biyu, amma ba zai iya tantance ko akwai wasu gawawwakin ba a cikin gidan.

Sai dai kakakin rundunar ‘Yan sandan Jahar ya musanta labarin sabon harin.

A cewar Magaji Majia babu wani sabon hari da aka kai a birnin Kano.

A makon jiya an kai wasu hare hare a birnin Kano da suka yi sandiyar mutuwar mutane 185, Al’amarin da yasa gwamnatin Jahar ta kafa dokar hana fita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.