Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu-Najeriya

Kotun Afrika ta Kudu ta kama Henry Okah na Najeriya da laifuka 13

Wata Kotu a Afrika ta kudu, ta samu Henry Okah, Dan Najeriya da laifuka 13 da ke da alaka da ayyukan ta’adanci, da suka hada da harin Bom da aka kai a Abuja, ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2010 da wasu jerin hare hare da aka kai a yankin Neja Delta a watan Maris.

Henry Okah Na Najeriya da aka cafke a kasar Afrika ta Kudu
Henry Okah Na Najeriya da aka cafke a kasar Afrika ta Kudu Reuters
Talla

Alkalin kotun Neels Claassen, yace ya gamsu da shaidun da aka gabatar masa akan wanda ake zargi.

Bayan kai harin ranar bukin cika shekaru 50 da samun ‘Yancin kan Najeriya, Kungiyar MEND da ke fafutikar ‘Yantar da yankin Neja Delta ta fito ta yi ikirarin kai harin.

An kwashe lokaci mai tsawo Kungiyar MEND tana kai hare hare a Yankin Neja Delta tare da garkuwa da Turawa da ke aiki a Kamfanonin hako man Fetir a Najeriya.

Gwamnatin Afrika ta Kudu tace ta cafke Okah ne karkashin dokar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da ta’addanci a Duniya.

Mista Okah wanda ya mallaki gidan kansa a kasar Afrika ta kudu, an taba yanke masa hukunci a kasar Angola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.