Isa ga babban shafi
Nigeria

An Cafke Dan uwan Heny Okah kan tashi bama baman Aubja

Jami'an tsaro a tarayyar Nigeria, sun kama Dan uwan shugaban kungiyar dake fafutukar Yantar da Yankin Niger Delta, Henry Okah, wanda ake zargi da tashin bama bamai a Abuja fadar gwamnatin kasar.Rahotanni sun ce an kama Charles Okah ne a garin Lagos, kuma ana zargin yana da hannu wajen taimakawa Dan uwan sa.A wata hira da kanfanin Dillancin labaran kasar Faransa, Henry Okah, ya bayyana zargin da ake masa a matsayin wasan yara.Okah ya danganta abinda yake faruwa da zabe mai zuwa, inda ya ce gwamnatin Nigeria na zargin sa cewar yana goyawa 'yan adawa baya. 

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.