Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta tura Bala Muhammad gidan yarin Kuje

Wata kotun Tarayya a Abuja Najeriya ta tura Bala Muhammad zama a babban gidan yarin Kuje kan tuhumarsa da aikata laifukan rashawa a lokacin da yana ministan Abuja.

Tsohon Ministan Abuja Bala Muhammad
Tsohon Ministan Abuja Bala Muhammad famouspeoplemagazine
Talla

Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ne ta maka tsohon ministan na Abuja a kotu kan cajinsa da aikata laifuka shida da suka kunshi sama da fadi da kudi Naira Miliyan 550.

Sannan ana zarginsa da rashin bayyana wasu kadarorin da ya mallaka. Amma Bala ya musanta dukkanin zargin.

Sai a ranar 12 ga Mayu ne Kotu za ta sake sauraren karar tsohon ministan inda za ta yanke hukuncin ba da shi beli.

Amma yanzu zai ci gaba da zama a gidan yarin Kuje har zuwa 12 ga wata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.