Isa ga babban shafi
Kano

An fara binciken masarautar Kano

Hukumar da ke sauraren koke-koken jama`a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a Najeriya ta ce ta fara sauraron bayanai daga wasu jami`an fadar Sarki Sanusi na biyu a binciken da ta kaddamar a kan yadda aka kashe kudaden masarautar.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu REUTERS/Joe Penney
Talla

Wasu al`ummar jihar ne suka gabatar da korafinsu kan masarautar ta Sarki Sanusi na biyu ga hukumar.

Kwamred Muhuyi Magaji shugaban hukumar ya shadiawa wakilin RFI Hausa Abubakar Isah Dandago cewa masarautar ta bayar da hadin kai a binciken da aka soma da jami’ai guda biyu.

A ranar 23 ga Maris ne hukumar ta kaddamar da bincike kan yadda masarautar Kano ta kashe kudade ba bisa ka’ida ba,

Kodayake fadar Sarki Sanusi ta bayyana cewa Naira biliyan 2.9 aka kashe sabanin biliyan 6 kudaden da ake zargin an yi facaka da su, a hidimar masarautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.