Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Muna iya musayar 'yan matan Chibok da fursunonin Boko Haram-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yace a shirye yake ya musanya ‘ya’yan kungiyar Boko Haram dake hannunsu da ‘yan matan sakandaren Chibok da mayakan suka yi garkuwa dasu.

Buhari da Amina Ali, daya daga cikin 'yan matan Chibok da ta kubuce daga hannun mayakan Boko Haram.
Buhari da Amina Ali, daya daga cikin 'yan matan Chibok da ta kubuce daga hannun mayakan Boko Haram. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Buhari yace zai baiwa kungiyar damar bayyana wadanda suke so su shiga tsakani dan tattaunawa da jami’an gwamnatin dan ganin an sako ‘yan matan kusan 200 dake hannun su.

Shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a yayin ziyararsa a kasar Kenya a yayin da yake ganawa da manema labarai.

A makon jiya iyayen ‘Yan matan na Chibok sun bukaci shugaban ya sauka daga kujerarsa idan ba zai iya ceto ‘ya’yan nasu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.