Isa ga babban shafi
Najeriya

An takaita wa Jami’an gwamnati hawa babbar Kujerar Jirgi

Gwamnatin Najeriya tace zata datse kudaden da ake kashewa ga manyan Jami’an gwamnati na hawa babbar kujera a jirgin sama domin yin amfani da kudaden ga ayyukan ci gaban kasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP via telegraph
Talla

Ma’aikatar kudi tace manyan jami’an gwamnati da ke hawa babbar kujera za su koma hawa karamar kujera don rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin Ma’aikatar kudin tace a karkashin tsarin za a samu rarar kudi sama da Naira Biliyan 13.88.

Sannan an bukaci ma’aikatun gwamnati su dinga yin taro a yankunansu domin rage kudaden jirgin da ake kashewa sannan daga yanzu sai sun nemi izini daga gwamnatin Tarayya kafin gudanar da wani taro a kasashen waje.

Najeriya dai na fuskantar matsalar tattalin arziki saboda faduwar farashin mai a kasuwar duniya. Kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawalin rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa tare da karkatar da tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.