Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mujuru ta kafa sabuwar Jam’iyya domin hamayya da ZANU PF

Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Zimbabwe Joice Mujuru ta kafa wata sabuwar Jam’iyya domin kalubalantar shugaba Robert Mugabe, mai dogon zamani.

Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Zimbabwe Joice Mujuru ta kafa wata sabuwar Jam’iyya domin kalubalantar shugaba Robert Mugabe
Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Zimbabwe Joice Mujuru ta kafa wata sabuwar Jam’iyya domin kalubalantar shugaba Robert Mugabe REUTERS
Talla

A yau Talata ne Mujuru ta kaddamar da jam’iyyar mai suna Zimbabwe People First Party a birnin Harare domin hamayya da Jam’iyyar ZANU PF ta Mugabe.

Tun samun ‘yancin kasar a 1980 Mugabe mai shekaru 92 ke shugabanci a Zimbabwe.

Kuma ana sa ran Mugabe zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2018, a yayin da kuma ake ta yawo da hankalin ‘yan kasar akan wanda zai gaje shi saboda tsufa da rashin koshin lafiya.

A lokacin da ta ke zantawa da manema labarai Mujuru ta kaucewa kalubalantar Mugabe, tana mai cewa shugabanta ne da dadewa.

Mujuru dai ta kasance mataimakiya ga Mugabe kuma ta shafe shekaru sama da 30 cikin masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar ZANU PF

A 2014 ne ZANU PF ta kore ta daga jam’iyyar bayan Matar Shugaba Mugabe ta zarge ta da yi wa Jam’iyyar zagon kasa tare da kokarin hambarar da mijinta daga madafan ikon Zimbabwe.

Masharhanta na ganin Kaddamar da sabuwar jam’iyyar babban kalubale ne ga ZANU PF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.