Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An haramta auren 'yan kasa da shekaru 18 a Zimbabwe

Babbar Kotun kasar Zimbabwe ta haramta yin auren yara ‘yan kasa da shekaru 18 maza da mata, matakin da ya kawo karshen auren kananan yara a kasar.Wannan dai ya farantawa ‘Yan rajin kare hakkin mata rai a kasar.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Kotun kundin tsarin mulki ya zartar da hukuncin haramta auren na ‘yan kasa da shekaru 18 a Harare bayan koken da wasu mata suka shigar a gabanta kan kuncin rayuwar da auren dole ya jefa su suna kanana.

Matan suna da shekaru 15 aka aurar da su. Kuma dalilin haka ne Zimbawe ta haramta auren kananan yara.

‘Yan rajin kare hakkin mata dai sun yaba da matakin wanda suka ce garkuwa ne ga mata da ake yi wa aure suna yara.

Abin da ya rage kuma yanzu shi ne Majalisar kasar ta fadi hukuncin da ya hau kan wanda ya saba dokar haramcin auren na ‘yan kasa da shekaru 18.

Hukumar Unicef da ke kula da yara kanana tace adadin auren yaran da ake yi a Afrika zai Ninka zuwa 2015. Wanda hakan kuma ke nuna kasar Zimbabwe ta fara daukar matakan rage yawaitar auren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.