Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Majalisar Zimbabwe ta amince da dokar tsaurara korar aiki

Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da wata sabuwar doka da ke tsaurara irin matakan da ya kamata a mutunta kafin korar mutum daga aiki.

Reuters/Philimon Bulawayo
Talla

Samar da dokar dai ya biyo bayan korar wasu ma’aikata dubu uku ne da aka yi a rana daya, bayan samun amincewar kotun kolin kasar a cikin watan yulin da ya gabata, kuma a cewar kungiyar kwadagon kasar.

Yanzu haka akwai wasu mutane sama da dubu 18 da gwamnatocin kananan hukumomi ke shirin kora daga aiki matukar dai ba a gaggauta samar da wannan doka ba.

A gobe alhamis ake saran majalisar dattawan kasar za su mikawa Shugaban kasar Robert Mugabe kudirin amincewa domin ya sanya hannu.

Rashin aikin yi dai na ci gaba da yiwa al’ummar Zimbabwe katutu tsawon shekaru, yayin da tattalin arzikin kasar ke tafiyar hawainiya.

Kamfannoni da Masana’antu da dama ne suka yi balaguro daga Zimbabwe zuwa kashe dake makwabtaka da su sakamakon halin da kasar ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.