Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An kori ma’aikata 20,000 a Zimbabwe a wata guda

Mutane kimanin 20,000 suka rasa ayyukansu tsakanin watan jiya zuwa yanzu a kasar Zimbabwe, wannan kuma ya faru ne sakamakon hukuncin kotu da ta ba kamfanoni damar korar ma’aikata karkashin dokar wa’adin kora na watanni uku.

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Zimabwe dai na fama da yawan masu zaman kashe wando, kuma Kamfanoni a kasar na fama da matsalar katsewar wutar lantarki, lamarin da ke gurgunta ayyukan ci gaban masana’antu a kasar.

Kungiyar kwadago a kasar ta bukaci gwamnati ta gaggauta daukar mataki domin kawo karshen matsalar rashin ayyukan yi a kasar.

A ranar 17 ga watan Yuli ne dai kotun koli a Zimbabwe ta amince da wa’adin kora na tsawon watanni uku, matakin da kuma ya budewa kamfanoni kofar korar ma’aikatansu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar kwadagon tace kimanin ma’aikata dubu ashirin kamfanoni suka kora cikin wata guda a Zimbabwe.

Kuma kungiyar ta yi gargadin akan adadin na iya karuwa idan har gwamnati bata dauki mataki ba.

Tuni dai shugaban kasar Robert Mugabe ya sha alwashin samar da ayyukan yi miliyan 2 ga ‘yan kasar bayan ya lashe zaben shugaban kasa a 2013.

A ranar juma’a kuma shugaba Mugabe ya bukaci a sauya dokar ma’aikta domin samar da sharadin da ya kunshi tursasawa kamfanoni masu zaman kansu ware kudade masu tsoka ga duk ma ‘aikacin da za su kora.

Yanzu haka majalisar kasar da ke hutu ta katse hutunta domin tattauna batun a ranar Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.