Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zan ci gaba da tilastawa turawa sayar da kamfanoninsu ga ‘yan kasa - Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya ce zai ci gaba da aiwatar da salon siyasar da zai tilastawa kamfanonin kasashen waje da ke cikin kasar sayar da hannayen jarinsu ga ‘yan asalin kasar. 

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Shugaban wanda ke gabatar da jawabi a gaban dumbin jami’an tsaro da ke gudanar da fareti a birnin Harare, ya ce “a halin yanzu da al’ummar kasar suka danka amanarsu a gare ni, babban abin da zan mayar da hankali a kai shi ne kammala aikin mayar da dukiyar kasa a hannun ‘yan kasa.”

Mugabe ya ce aiwatar da wannan manufa, na daya daga cikin manyan ginshikai na gwagwarmayar da suke yi domin ‘yantar da kasar, inda kuma ya ce ba za a ci gaba da zura ido kamfanonin kasashen ketare na yin kane-kane kan dumbin arzikin kasar ba.

Har ila yau shugaban na Zimbabwe dan shekaru 89 a duniya, a fakaice ya soki lamirin abokin hamayyarsa na siyasa wato Morgan Tsavanguirai inda yake cewa “na yi matukar mamaki dangane da yadda wasu ‘yan kasa ke hada baki da kasashen yamma domin cutar da Zimbabwe,’’

Wannan dai shi ne karo na biyu da Robert Mugabe ke gabatar da jawabi a bainar jama’a tun bayan nasarar da ya yi a zaben shugabancin kasar na ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata, zaben da har yanzu kasashen Yamma ke nuna shakku dangane da sahihancinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.