Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Tsvangirai ya shigar da kara domin kalubalantar zaben Mugabe

Lauyan da ke kare Jam'iyyar adawa ta Morgan Tsvangirai ya shigar da kara a kotun kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka bayyana sunan Robert Mugabe a matsayin wanda ya lashe zaben.

Morgan Tsvangirai, Babban mai hamayya da Mugabe a kasar Zimbabwe
Morgan Tsvangirai, Babban mai hamayya da Mugabe a kasar Zimbabwe REUTERS/ Philimon Bulawayo
Talla

Mai Magana da yawun Jam’iyyar adawar ne ya shaidawa manema labarai bayan sun shigar da karar a harabar kotu.

Tsvangirai da Jam’iyyarsa ta MDC sun ce zaben da aka gudanar a ranar 31 ga watan Yuli yana cike da kura-kurai da kuma magudi da aka tabka wanda suka bukaci a soke zaben.

Hukumar Zaben Zimbabwe tace Mugabe ya lashe zaben ne da rinjayen kuri’u kashi 61 fiye da Tsvangirai wanda ya samu kuri’u kashi 34.

Amma masu sa ido a zaben na ckin gida sun ce akwai matsala a zaben kamar yadda kasashen yammaci suka bayyana damuwa ga sakamakon zaben.

Amurka da Birtaniya sun ce an yi magudi, yayin da Austalia ta nemi a sake gudanar da zaben baki daya.

Amma kungiyar Tarayyar Afrika a ta bakin babban wakilinta Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo tace an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Yanzu haka dai shugaba Mugabe zai jira har sai lokacin da Kotun kundin tsarin mulki ta yanke hukunci kafin a rantsar da shi.

Wannan ne kuma karo na uku da Tsvangirai mai shekaru 61 ke shan kashi a hannun Mugabe mai shekaru 89 a zaben Zimbabwe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.