Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An kammala yakin neman zabe a Zimbabwe

A Zimbabwe an kawo karshen yakin neman zaben shugabancin kasar da za a gudanar gobe laraba, zaben da zai hada ‘yan takara biyu Robert Mugabe da ke kan karagar mulki tun a shekarar 1980 da kuma babban mai hamayya da shi kuma firaministan kasar Morgan Tsavangirai.

Hotunan 'Yan takarar zaben shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da Morgan Tsvangirai,
Hotunan 'Yan takarar zaben shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da Morgan Tsvangirai, REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Tuni dai Robert Mugabe ya yi alkawalin cewa zaben zai gudana a cikin kyakkyawan tsari, to sai dai jam’iyar MDC ta Morgan Tsangirai ta bakin David Colatart mai Magana da yawunta, suna da shakku a game da manufar Mugabe.

Morgan Tsvangirai ya bukacin mutanen Zimbabwe su zabe shi a matsayin shugaban kasa domin samar da ci gaba mai dorewa.

A zaben 2008 Morgan Tsvangirai shi ne ya lashe zagaye na farko amma daga baya ya fice kafin a shiga zagaye na biyu saboda mutuwar magoya bayan shi kimanin 200.

Tun a ranar Lahadi ne shugaba Mugabe ya kammala yakin neman zaben shi tare da yin alkawalin gudanar da karbabben zabe.

Masu sa ido a zaben sun ce alamun gudanar da ingantaccen zabe baya da yawa, kodayake sun ce babu wani tashin hankali da aka samu gabanin zaben.

Akwai dai fargabar samun rikici saboda rikicin da aka samu a lokacin da Jami’an tsaro suka kada kuri’unsu mako biyu da suka gabata. Daruruwan ‘Yan sanda da Sojoji ba su samu damar kada kuri’a ba saboda karancin kayan zabe.

Robert Mugabe ya kwashe tsawon shekaru 33 yana mulki a kasar Zimbabwe kuma Morgan Tsvangirai shi ne babban mai adawa da shi a zaben da za’a gudanar a ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.