Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Jam’iyyar Mugabe ta yi ikirarin lashe zaben Zimbabwe

Jam’iyyar shugaba Robert Mugabe ta ZANU PF ta yi ikirarin lashe zaben shugaban kasar Zimbabwe, inda kuma bangaren Firaminista Morgan Tsvangirai na Jam’iyyar MDC ke koken an tabka magudi.

Wani Dan sanda yana kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Zimbabwe
Wani Dan sanda yana kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Zimbabwe REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A tsarin dokar Zimbabwe,  bayyana sakamakon zabe sabanin hukuma laifi ne, kuma ‘Yan sanda sun sha alwashin hukunta duk wanda suka kama yana bayyana sakamakon zabe.

Amma wata majiyar gwamnatin Mugabe da ta nemi a sakaye sunanta tace Jam’iyyar ZANU PF ce ke kan gaba.

A zaben shugabancin kasar da aka gudanar a kasar Zimbabwe, ana hamayya ne tsakanin ‘Yan takara biyu shugaba mai ci Robert Mogabe da kuma Firaministansa Morgan Tsvangirai. An samu fitowar dimbin jama’a a lokacin wannan zabe da kasashen duniya ke bi sau da kafa domin ganin yadda za ta kaya.

Mugabe mai shekaru 89, ya kwashe shekaru sama da 30 yana shugabanci a Zimbabwe, shugaba mafi tsufa a karagar mulki a Afrika, amma abokin hamayyar shi Morgan Tsvangirai yana fatar wannan zaben zai tabbatar sauyi a kasar.

Babu dai wani labarin tashin hankali da aka samu a lokacin gudanar da zaben sai dai kuma ba a san me zai biyo baya ba idan aka bayyana sakamakon zaben.

Tuni dai bangaren Morgan Tsvangirai suka yi zargin an tabka magudi.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo wanda ya ke jagorantar tawagar wakilai 69 masu sa idanu daga kungiyar Tarayyar Afrika ya fadi da bakinsa cewa zaden an yi shi cikin kwanciyar hankali, kuma babu magudi.

Amma Firaminista Morgan Tsvangirai da ke takaran Shugabancin kasar ya soki tawagar Kungiyar Tarayyar Afrika saboda nunawa duniya cewa an yi shiri a zaben da aka gudanar.

Bangaren Morgan Tsvangirai suna zargin an shirya magudi saboda yadda aka jinkirta gabatar da sunayen wadanda za su jefa kuri’a sai a ranar zabe.

Sai dai kuma Daraktan Hukumar zabe na kasar  Pedzei Puhanya yace zaben ya yi kyau, yana mai ikirarin jinkirin da aka samu ba wani abin a yi korafi ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.