Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Amurka da Birtaniya sun kalubalanci zaben Zimbabwe da Mugabe ya lashe

Hukumar zabe a Zimbabwe ta bayyana sunan Shugaba Robert Mugabe a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, yayin da babban mai adawa da shi Morgan Tsvangirai, ya sha alwashin kalubalantar sakamakon zaben, wanda Amurka tace an yi magudi.

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe,
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Mugabe mai shekaru 89 ya kwashe tsawon shekaru 33 yana mulki a Zimbabwe tun samun 'yancin kasar a 1980, kuma yanzu zai kara wasu shekarun ne a wa’adi na bakwai, bayan ya kada Morgan Tsvangirai da suka dade suna adawa.

Sakamakon zaben yace Jam’iyyar ZANU PF ta Mugabe ta lashe kashi 61 ne cikin 100 tare da samun rinjaye a Majalisa, yayin da Jam’iyyar Tsvangirai, ta samu kuri’u kashi 34.

Akwai  sabani ra’ayi da aka samu daga masu sa ido a zaben Inda babban mai sa ido a tawagar kungiyar kasashen Afrika tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yace an gudanar da zaben cikin tsabta ba tare da magudi ba.

Amma a wata sanarwa da ta fito daga sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry, Amurka tace an yi magudi.

A nata bangaren Kungiyar Tarayyar Turai tace akwai kura-kurai a zaben tare da bayyana fargaba ga ci gaban demokradiya a kasar.

Amma kungiyar ci gaban kasashen Kudancin Afrika ta SADC tace zaben an gudanar da shi cikin lumana ba tare da fitowa fili tace ko an yi magudi ba.

Tuni dai bangaren Mugabe suka yi watsi da duk wani zargi da ake yi sun tabka magudi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.