An zabi Kabore Shugaban kasar Burkina Faso
Hukumar Zabe a Kasar Burkina Faso ta tabbatar da Roch Marc Christian Kabore a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Lahadi bayan ya samu rinjayen kuri’u a zagaye na farko.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kabore wanda tsohon Firaminista ne a kasar ya lashe zaben shugaban kasar ne da kuri’u kashi 54.49, yayin da Zaphirin Diabre ya zo a matsayi na biyu da yawan kuri’u kashi 29.65.
Zaben Burkina Faso dai ya kankama ne ba tare da wani tashin hankali ba, duk da an shafe shekara guda kasar na cikin rudanin siyasa, bayan kawo karshen mulkin Blaise Compaore.
Daga Ouagadougou Abdulkarim Ibrahim Shikal wanda ya sa ido a zabenya aiko da rahoto.
Rahoto: Kabore ya lashe zaben Shugaban kasar Burkina Faso
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu