Ana zaben shugaban kasa a Burkina
Al’ummar kasar Burkina Faso na gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisun dokoki a yau Lahadi inda ‘Yan takara 14 ke neman shugabancin kasar.
Wallafawa ranar:
Da sanyin safiya misalin karfe 6 aka bude runfunar zabe inda al’ummar kasar Miliyan 5 ke da ‘yancin kada kuri’a a zaben da ake gani mafi muhimmaci a Burkina faso bayan boren da ya kawo karshen mulkin shekaru 27 na Blaise Compaore.
Mutane 14 ke takarar shugabancin kasa, yayin da wasu daruruwa ke takarar neman shiga majalisar dokokin kasar mai kujeru 127.
Ana sa ran kammala zaben da misalin karfe 6 na yamma. Hukumar zaben kasar tace zuwa Litinin zata fitar da sakamako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu