Yakin neman zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisa
Da misalign karfe 12 na daren yau asabar ake kaddamar yakin neman zaben shugabancin kasa zagaye na farko da na ‘yan Majalisar dokoki a Burkina Faso, a yunkurin da ake na sake maido kasar kan turbar dimokuradiyya.
Wallafawa ranar:
Burkina Faso dai ta share tsawon shekara daya a karkashin gwamnatin rikon kwarya, bayan da boren al’ummar ya yi sanadiyyar faduwar gwmanatin Blaise Compaore wanda ya mulkin kasar shekaru 27.
Hakazalika yunkurin da wasu sojoji wadanda ga alama ke biyaya ga tsohon shugaban na kwace mulki a watannin da suka gabata ya ci tura, sakamakon jajircewar al’ummar kasar da kuma sauran kasashen duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu