Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Ana jiran sakamakon zaben Burkina Faso

Al’ummar kasar Burkina Faso na dakun sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘Yan majalisu zagaye na farko da aka gudanar a ranar Lahadi, zabe na farko da aka gudanar a kasar tun kawar da gwamnatin Blaise Compaore.

Ana kidayar Kuri'u a zaben shugaban kasa da na 'Yan Majalisun dokoki a Burkina Faso
Ana kidayar Kuri'u a zaben shugaban kasa da na 'Yan Majalisun dokoki a Burkina Faso REUTERS/Joe Penney
Talla

Yanzu haka ana ci gaba da kidayar kuri’un da aka kada

Masu sa ido na kasashen Afrika da na Turai sun yaba da yadda aka gudanar da zaben inda ‘Yan takara 14 ke neman kujerar shugaban kasa.

Hukumar zaben kasar tace ana iya smaun sakamakon zaben a yau Litinin.

Abdoulkarim Ibrahim Shikal da ke sa ido a zaben daga Ouagadougou ya aiko da rahoto.

01:33

Rahoton Abdulkarim daga Ouagadougou

Abdoulkarim Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.