Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Masu sa ido a zaben Burkina Faso sun soma isa kasar

A jibi lahadi al’ummar Burkina faso za su gudanar da zaben shugaban kasa irinsa na farko cikin shekaru 30, zaben da ake fatan ya bude sabon babin sauyi a kasar, data fada cikin tashin hankali tun bayan hambarar da gwamnatin Blaise Compaore. 

Tutar Burkina Faso dauke da hoton mutumen da zai lashe zaben kasar
Tutar Burkina Faso dauke da hoton mutumen da zai lashe zaben kasar RFI
Talla

Karo na farko a cikin shekaru kusan 30 da kasar Burkina Faso mai yawan al’umma miliyan 20 zata gudanar da zaben shugabanci kasa bayan hambarar da Gwamantin Blaise Compaore daya shafe tsawon shekaru 27 kan karagar mulkin kasar

Compaore dake hijira a kasar Cote D’Ivoire ya karbe Shugabancin kasar ne bayan juyin mulkin da yayi wa Thomas Sankara a shekara ta 1987.

A cewar shugaban rikon kwaryar kasar Michel Kafando gwamnati ta dau matakan tabbatar da cewa anyi zaben kasar a cikin gaskiya da lumana kan tafarkin dokokin demokradiya.

Mutane 14 ne dai ke takarar wannan kujera, hukumomin ta bakin ministan cikin gida Alain Zagre jami’an tsaro 25.000 za bada kulawa ta musaman domin kare lafiya al’uma a lokaci zaben.
Rahotani daga babban birni kasar Ouagadougo na nuni da cewa masu sa ido a wanan zabe sun soma isa kasar ta Burkina Faso.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.