Isa ga babban shafi
Najeriya

NNPC zai yi maganin barayin mai

Kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya bayyana cewa zai fara amfani da jiragen da ke tuka kansu domin sa ido ga shige da ficen jiragen ruwa da ke dakon fetir a kasar.

Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya
Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya RFI
Talla

Shugaban Kamfanin Ibe Kachikwu ne ya bayyana daukar matakin a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wani taron Gulf Guinea a Abuja.

Kachikwu ya ce za su yi maganin barayin fetir da fasa butun mai ta hanyar amfani da jirage masu tuka kansu a iyakokin ruwan Najeriya.

Kuma Shugaban Kamfanin ya ce nan da ‘yan watanni ne suke fatar soma aiwatar da matakin.

A cewarsa, tsakanin watan Yunin 2014 zuwa 2015 an kai wa bututun mai kusan 4,000 hari a sassan Najeriya, kuma kimanin mutane 350 aka kashe da suka hada da ma’aikatan Mai da ‘Yan sanda da kuma mutanen yankin Neja Delta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.