Buhari ya nada sabon shugaban kamfanin NNPC
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Emmanuel Ibe Kachikwu a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na NNPC bayan tube shugabanin gudanarwar kamfanin tuntuni.
Wallafawa ranar:
Sanarwar nadin Kachikwu ta fito ne daga Femi Adeshina, Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari.
Kachikwu dai tsohon mataimakin shugaban kamfanin mai ne na Exxon-Mobil mai kula da nahiyar Afrika, kuma dan asalin Jihar Delta ne mai arzikin mai.
Kachikwu kwararre ne a bangaren makamashi wanda ya yi karatu a Jami’ar Harvard.
Bayan nadinsa, Kachikwu ya yi alkawalin gudanar da aiki da gaskiya tare da tunkarar kalubalen da ke gabansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu