Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya rusa hukumar zartarwar NNPC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rusa hukumar zartarwa ta kamfanin mai na kasar NNPC a yau juma’a. A wata wasika da shugaban ofishin ma’aikata na Tarayyar Danladi Kifasi ya sanya wa hannu, Buhari ya jinjina wa mamabobin hukumar gudanarwar da aka sallama.

Kamfanin mai na NNPC.
Kamfanin mai na NNPC. Getty Images/Suzanne Plunkett
Talla

Kamfanin na NNPC dai shi ne ke kula da batutuwan da suka shafi mai da iskar gaz da kasar ke fitarwa, kuma su ne manyan hanyoyin da kasar ke samun kudaden shiga.

Ministan kula da man fetir ne ke jagorantar hukumar Zartarwar Kamfanin NNPC wanda rashawa ya yi wa katutu musamman bayan zargin bacewar kudi dala biliyan 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.