Za a bi didigin kudin man Feturin da NNPC ya karkatar
Gwanan Jihar Edo da ke Najeriya Adams Oshiomhole ya ce a cikin shekaru uku kanfanin man kasar NNPC ya tara kudaden da suka kai trillion sama da 8 amma kuma trillion 4 da kusan rabi ya saka asusun gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
Gwamnan ya ce bankin ya soke sama da trillion 3 a aljihun sa inda ya kashe su ba tare da amincewar gwamnati ba.
Oshiomhole ya kuma tabbatar da cewar an kwashe sama da Dala biliyan 2 daga asusun rarar man fetur a watan Nuwamba na bara ba tare da amincewar majalisar tattalin arzikin kasar ba.
Gwamnan ya ce yanzu haka sun kafa kwamitin mutane 4 dan nazarin takardun bayanan kanfanin man dan gano gaskiyan abinda ya kun sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu