Isa ga babban shafi
Ebola

WHO ta bayar da umurnin a fara amfani da maganin Ebola

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta amince a fara amfani da maganin gwaji da aka samar domin yakar cutar Ebola da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000 bayan kamfanin ZMapp da ya samar da maganin ya aika shi zuwa kasashen yammacin Afrika da cutar ta zama alakakai.

Wani Allon sanarwa akan Cutar Ebola da Jami'an shige da fice suka kafa a kasar Liberia domin tantance mutane
Wani Allon sanarwa akan Cutar Ebola da Jami'an shige da fice suka kafa a kasar Liberia domin tantance mutane REUTERS/Stringer
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bukaci gwamnatocin kasashen duniya su dai na fargaba kan cutar Ebola yayin da ya nada wani masani Dan kasar Birtaniya David Nabarro a matsayin Jakadan da zai sa ido kan yadda za’a magance yaduwar cutar.

Wannan kuma na zuwa ne bayan Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS tace wani jami’inta Jatto Asihu Abdulkadir ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Ebola. Kungiyar tace jami’in yana cikin mutanen da suka yi mu’amula da Patrick Sawyer mutumin Liberia da ya kai cutar Ebola mai yin kisa a Najeriya.

Cutar Ebola dai ta zama annoba a yammacin Afrika inda ta kashe mutane da dama a Liberia da Guinea da Saliyo.

Masana sun ce Maganin gwajin da aka samar zai dan dauki lokaci kafin sake sarrafa wasu daga cikinsu saboda yanzu haka bai da yawa ga wadanda ake da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.