Isa ga babban shafi
Najeriya

An tsaurara Tsaro a Abuja saboda taron tattalin arziki

Hukumomin Najeriya sun girke jami'an tsaro kimanin 6,000 domin tabbatar da tsaro wajen taron tattalin arzikin duniya da aka bude a birnin Tarayya Abuja. An bude taron ne cikin fargabar matsalar tsaro bayan wasu hare haren bama bamai da aka kai a Nyanya a Abuja.

'Yan sanda suna gudanar da bincike a inda aka kai harin bom a Nyanya a Abuja
'Yan sanda suna gudanar da bincike a inda aka kai harin bom a Nyanya a Abuja REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Amma maganar sace ‘Yan mata sama da 200 shi ne ya karkatar da hankalin duniya fiye da taron da za’a gudanar a karon farko a Najeriya.

Firimiyan China Li Keqiang yana cikin manyan shugabannin kasashen duniya da suka halarci zaman taron tare da wakilan manyan kamfanoni da masana’antu a sassan kasashen duniya.

01:17

An tsaurara Tsaro a Abuja saboda taron tattalin arziki

Kabir Yusuf

An tsaurara matakan tsaro a tashar jirgin sama a Abuja da kuma ciki da wajen birnin.
Kuma daga yau Laraba zuwa Juma’a an rufe ofisoshin gwamnati da makarantu saboda taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.