Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta dauki alhakin sace 'yan matan Chibok

Kungiyar Jama’atul Ahlil Sunnah Lil Da’awati wal Jihad, wacce aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ke da alhakin sace ‘yan mata dalibai a garin Chibok da aka yi kusan makwanni uku da suka gabata a jihar Bornon Najeriya.

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau (Boko Haram/AFP)
Talla

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani hoton bidiyo da ta fitar, inda Shugabanta, Abubakar Shekau ya kwashe mintina 57 yana magana kan batutuwa da dama ciki har da batun sace ‘yan matan.

Shekau ya yi jawabin nashi ne sanye da rigar soja, da wani jan wando, hade da wata jar hular sanyi da kuma bindiga rataye a wuyansa, inda ya jaddada cewa, su suka sace ‘yan matan, ya kuma kara da cewa za su sayar da su a matsayin bayi.

“Ni na kama ‘yan matan naku, zan sayar a kasuwa, wallahi, akwai kasuwa na na sayar da mutum.” Inji Shekau, wanda ya yi magana da harshen Hausa da larabci da kuma turanci.

Har ila yau a cikin hoton bidiyon, Shekau wanda ya ke zagaye da wasu mutane shida da suka rufe fuskokinsu, hade da takunan yaki a bayansa, ya yi kakkausar suka ga tsarin mulkin dimokradiyya da kuma karatun boko, yana mai jaddada cewa zai aurar da mace ‘yar shekara 12 da kuma ‘yar shekara tara.

“Shekaranta 12 zan mata aure, yarinya shekaranta tara zan mata aure.” Shekau ya kara da cewa.

Wannan hoton bidiyo ya bayyana ne kasa da sa’o’i 24, bayan da Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da wasu kafofin yada labarai, inda ya sha alwashin za cewa za su ceto ‘yan matan, su kuma mika su ga iyalansu.

Akalla sama da ‘yan mata dalibai 200 aka sace a garin na Chibok, koda yake rahotannin baya baya nan na cewa adadin ya karu yayin da hukumomi ke fitar da bayanai masu karo da juna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.