Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Sojoji suna son a dakatar da Gwamnonin Arewa Uku

Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa taron Majalisar Tsaron kasa da za'a gudanar ranar Laraba mai zuwa zai duba yiwuwar dakatar da Gwamnonin Jihohin Adamawa da Borno da Yobe, don kaddamar da dokar ta-baci gaba daya, wanda wannan mataki ne na dakatar da shugabannin dimokradiya a yankin na arewa maso gabaci da ke fama da hare haren mayakan Boko Haram.

Sojojin Najeriya suna binciken wani sansanin mayakan Boko Haram a Kirenowa
Sojojin Najeriya suna binciken wani sansanin mayakan Boko Haram a Kirenowa AFP Photo
Talla

Jaridar Leadership da ake bugawa a arewacin kasar ta ruwaito wani Babban jami'in sojin kasar na zargin manyan 'Yan siyasa a Jihohin uku da kuma Dattawan Yankin da hana ruwa gudu ga aikin da suke, tare da bayyana bukatar kawar da daukacin Gwamnonin yankin da Majalisa da shugabannin kananan hukumomi domin fuskantar aikin wanzar da tsaro gadan gadan.

Wannan kuma ya Shafi Gwamnan Jahar Adamawa Murtala Nyako da Gwamnan Jahar Borno Kashin Shettima da ke adawa da gwamnatin Jam'iyyar PDP ta Goodluck Jonathan.

Majiyar tsaron tace sun bayar da shawarar yin haka, saboda zagon kasa da Gwamnonin da wasu 'Yan siyasa ke yi ga aikinsu wajen yaki da ta'adanci, kamar yadda Jaridar Leadership ta ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.