Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun janye ikirarin kubutar da matan da aka sace

Rudunar Sojin Najeriya ta janye ikirarin sun kubutar da Dalibai mata 129 da’Yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka sace a garin Chibok da ke cikin Jahar Borno bayan gwamnatin Jahar da Shugaban Makarantar yaran sun karyata ikirarin.

Babban hafsan Sojin Najeriya Laftanal Janar Kenneth Minimah
Babban hafsan Sojin Najeriya Laftanal Janar Kenneth Minimah Informationnigeria
Talla

A jiya alhamis ne kakakin rundunar Sojin ta Najeriya Chris Olukolade ya yi ikirarin sun kubutar da matan kuma takwas kawai daga cikinsu suka rage a hannun ‘Yan bindigan da suka sace su a Chibok.

Kuma a jiyan ne shugabar Makarantar Asabe Kwambura ta karyata ikirarin na Sojin Najeriya tare da gasgata kalaman Gwamnan Jahar Borno Kashin Shettima wanda yace 14 daga cikin matan ne suka tsere.

A ranar Litinin ne wasu ‘Yan bindiga suka abka makarantar Sakandare suka sace Matan da suka je rubuta Jarabawa a lokacin da mutanen Najeriya ke juyayin kisan mutane 75 a harin bom da aka kai a Nyanya a Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.