Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi yasar kasa amma akwai wasu kauyuka masu Guba a Zamfara

Gwamnatin Najeriya tace ta kammala aikin kwashe kasar da ke dauke da guba a kauyuka Takwas na Jahar Zamfara sanadiyar aikin hako Zinari, amma yanzu akwai wasu kauyuka da dama da aka gano akwai guba wadanda ke bukatar kulawar gaggawa.

Wani yana fasa Dutsi a wajen sarrafa tace zinari a kauyen Bagega Jahar zamfara a Najeriya da ke fama da matsalar Gubar Dalma
Wani yana fasa Dutsi a wajen sarrafa tace zinari a kauyen Bagega Jahar zamfara a Najeriya da ke fama da matsalar Gubar Dalma RFI/Awwal Janyau
Talla

A shekarar 2010 ne aka gano Gubar Dalma a Jahar Zamfara, kuma kungiyar likitocin Medecins Sans Frontieres tace wannan ita ce matsala mafi muni da aka samu, bayan mutuwar akalla yara kimanin 400.

A ranar 15 ga watan Yuli ne aka kammala aikin yashe kasa mai dauke da guba a kauyen Bagega, wanda shi ne gari mafi muni cikin kauyukan da gubar ta shafa.

Kauyukan da gubar ta shafa sun hada da ‘Yar Galma da Bagega da Duza da Sunka da Tungar Daji da Abare da Tungar Guru da Dareta.

Rayuwar dubban kananan yara ne suka fuskanci barazana bayan da aka samu tsaikun fitar da kudi daga gwamnatin Najeriya domin gudanar da aikin yashe kasar mai guba.

Ministan kula da muhalli Hajiya Hadiza Mailafiya tace sun cika alkawalin da suka dauka na kammala aikin, bayan fitar da kudaden a watan Janairun bana.

“Gidaje sama da 400 ne aka karkare kasar da ke cikin dakunan mazauna Bagega tare da kwashe kasar mai guba zuwa wajen gari” inji Hajiya Hadiza.

03:48

Rahoto: Wasu Mazauna Bagega sun ce ba a yashe kasar gidansu ba

Amma a ziyarar da sashen hausa na Rediyo Faransa ya kai a kauyen Bagega, wasu mazauna garin sun yi koken ba a shiga wasu dakunansu ba.

“Daga cikin daki 10 an yashe guda biyu amma saura an dauko kasa ne aka zuba ba tare da yashe kasa da ke dauke da guba ba” inji Adamu Tsiko wani mazauni Bagega.

Uban Kasar Bagega Alhaji Haruna yace babu wanda ya zo da koken ba a yashe kasar gidansa ba amma ya shaidawa RFI Hausa cewa akwai wasu ramu da ba a cike ba.

Kamfanin Terra-Graphics ne suka yi aikin na kwashe kasar mai dauke da guba a kauyukan Zamfara kuma Shehu Anka yana cikin wadanda suka jagoranci aikin, yace sun yi amfani ne da na’ura kuma duk gidan da suka tsallake babu guba a ciki.

Aikin hakowa da sarrafa tace zinari har yanzu ba a fasa ba a kauyukan Zamfara duk da hasarar rayukan kananan yara da aka samu.

Nicole Langer Jami’ar kiyon lafiya ta Likitocin Medecins Sans Frontieres, tace yara 2304 suke kula da lafiyarsu a yanzu wadanda ke dauke da Gubar Dalma a Zamfara, kuma yaran sun hada da wadanda ke karbar magani da kuma wadanda aka auna jininsu da aka gano suna dauke da gubar.

Tun farko da aka samu barkewar annobar Gubar Dalma an yi tunanin ciwon bakon dauro ne da zazzabin cizon sauro, kafin likitocin su dauki samfarin jinin yaran zuwa kasar Jamus inda aka gano gubar dalma ce.

Yanzu an samu raguwar adadin yaran da ke mutuwa zuwa kashi 2.8 sabanin shekarun baya, kamar yadda Nicole ta shaidawa RFI Hausa.

03:21

Rahoto: Babu tabbas ga makomar rayuwar yaran da guba ta shafa a Zamfara

Amma a kauyukan da Gubar Dalmar ta shafa akwai yara da dama da suka samu tabin hankali da makanta da mutuwar jiki.

A kullum akan dauki jinin yaran domin auna mizanin gubar da ke jikinsu ko ta ragu ko kuma ta karu, amma likitocin sun ce akan kwashe shekaru da yawa kafin yaran da ke dauke da gubar su warke.

Sai dai wani mataki da masu aikin hako Zinarin a Zamfara suka ce sun dauka shi ne na kauracewa shigowa da kayan aikinsu a gidajensu domin kare lafiyar ‘yayansu.

Akwai kungiyoyin masu zaman kansu da ke ci gaba da aikin wayar da kai ga hanyoyin kaucewa yaduwar matsalar da magance ta, amma Cibiyar Inganta rayuwar jama’a ta CENCEX ta bukaci a biya iyayen yaran da suka mutu diyya domin akwai cin zarafi a ciki.

Adamu kwatarkwashi shugaban kungiyar CENCEX yace a matsayinsu na Kungiyoyi masu zaman kansu suna kallon matsalar Gubar Dalma ta hanya guda uku, hanyar Lafiya da bata Muhalli da kuma hanyar cin zarafi wanda ya shafi rashin kare hakkin Bil’adama.

“Mutanen nan ‘yan kasa ne, ‘Yan Najeriya ne, hakkin Gwamnati ne ta basu ruwan sha da magani da abinci amma abin kunya shi ne likitocin Medecins Sans Frontieres ne kawai ke kula da lafiyarsu”, a cewar Mista Adamu.

“ Yau idan likitocin nan suka fice ba mu san yadda makomar wadannan yaran za ta kasance ba a Zamfara”.

Akwai dai kudi Naira Miliyan Dari Takwas da Talatin da Bakwai da gwamnatin Najeriya ta fitar domin gudanar da ayyuka uku a Zamfara, bangaren Lafiya da Muhalli da kuma bangaren hako albarkatun kasa, amma kungiyar CENCEX tace sun bi hanyoyin da aka kashe kudaden.

Mista Adamu yace suna jiran su ga lokacin da Ma’aikatar lafiya zata fara aikin kula da lafiyar mutanen Zamfara domin akwai kudi fiye da Naira Miliyan 200 da suka karba.

“Mun bi kididdiga, kuma mun gano ma’aikatar Muhalli ta kashe akalla kashi 95 wajen yashe kasa mai guba a kauyukan Zamfara amma ba mu san me ake jira da sauran kudaden da Ma’aikatar hako ma’adinai suka kashe ba”.

Yanzu haka dai babu wasu Jami’an Kiwon lafiya daga gwamnatin Tarayya ko na Jahar Zamfara da ke aiki tare da Likitocin Medecins Sans Frontieres wajen kula da lafiyar yaran da gubar Dalma ta shafa a Jahar Zamfara.

Amma kwamishinan Lafiya Muhammad Kabir Janyau yace su suka fara gano gubar Dalma a Zamfara kuma gwamnatin Jaha tana iya kokarinta.

Kwamishinan ya karyata zargin da Kungiyoyi masu zaman kansu ke yi, yana mai cewa akwai Jami’ansu da ke aiki tare da Likitocin MSF a kauyukan Zamfara.

“Ba maganar yau ba idan ma tun jiya ne Medecins Sans Frontieres za su fice su tafiyarsu, domin ma’akatanmu da su ake aiki kuma muna da cibiya da mu ke bincike bincikenmu” a cewar Kwamishinan.

Kwamishinan kuma ya soki alkalumman da likitocin MSF suka bayar akan adadin mutanen da suka mutu.

“Kauyen da suke Magana duka adadin mutanen kauyen nawa ne? Mutane Shinge ne da za’a ce mutane 400 sun mutu”.

Duk da an kammala aikin yashe kauyukan da gubar ta shafa guda Takwas amma akwai wasu kauyuka da bincike ya gano suna dauke da guba. kusan 30 a yankunan Anka da Maru da Bukuyyum da kuma Gusau.

Dakta Ahmed Keku tsohon babban jami’in kula da lafiyar al’umma a jahar Zamfara yace sun gano kauyuka 36 masu dauke da guba a zamanin shi.

Matsalar Gubar Dalma a Zamfara

A wani sakamakon bincike da Sashen Hausa na Rediyo Faransa ya samu daga Nasir Tsafe Jami’in cibiyar binciken Gubar Dalma karkashin ma’aikatar Lafiya a Jahar Zamfara, binciken yace akwai wasu kauyuka a yankin Anka guda hudu da ke bukatar Kulawar gaggawa, da suka hada da Gobirawa da Kirsa da Tumani.

A yankin Gusau akwai kyauka guda hudu, da suka hada da Janyau Takama da Nasarawa GRA da Unguwar Danbaba da ake kira Tsunami da ‘Yar Mangwarora. A Maru akwai kyauka guda hudu, Kadauri da Kurar Mota da Malele da Tashar Gambo wanda hakan ke bukatar gwamnatin Najeriya ta sake lale.

Kungiyar Likitocin MSF tace za ta dauki lokaci kafin maka’aikatanta su fice daga Zamfara amma Wata matsala kuma da ake samu shi ne daga iyaye na rashin kai yaran Asibiti domin karbar magani.

Akwai dai bukatar ci gaba da aikin wayar da kai da kuma bin matakan da suka dace wajen aikin hako zinari, amma a Najeriya sai abu ya yi tsanani sannan ake bin hanyoyin magance shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.